What's New

Small bug fixes and several improvements

App Description

Al Kur'ani (Quran in Hausa)

Musulunci shine addinin da mafiya yawan Hausawa suke bi. Kimanin kaso 90 ne na Hausawa suke bin addinin musulunci. Ma'anar Musulunci shine "Mika wuya ga kadaituwan Allah (SWT) cikin abubuwan da ya kebantu dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai." Allah (SWT) shi ya aiko Annabi Muhammadu (Yabo da Amincin Allah su Tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma. Yanzu haka, akwai fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari biyar a fadin duniya.

Tarihin Addinin Musulunci
Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa [[Annabi Ibrahim], da Annabi Musa, da Annabi Isa, alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al'ummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin al'ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma'ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).

iPhone Screenshots

(click to enlarge)

Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 1 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 2 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 3 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 4 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 5

iPad Screenshots

(click to enlarge)

Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 6 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 7 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 8 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 9 Al Kur'ani (Quran in Hausa) screenshot 10

App Changes

  • July 19, 2015 Initial release
  • November 09, 2015 New version 1.1
  • June 22, 2016 New version 1.2